
Gwamnatin jihar Borno ta ce ta fitar da naira miliyan 611.9 domin biyan tallafin karatu domin dalibai marasa galihu a manyan makarantu.
Babban Sakataren na Hukumar bayar da Tallafin Karatu ta jihar Borno, Bala Isa ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a wani taron manema labarai a Maiduguri.
“Muna da albishir ga daliban Borno, mai girma Gwamna Babagana Zulum ya amince da fitar da kudi N611.9m domin biyan alawus alawus din dalibai na 2021/22.
“Wannan ya yi daidai da kudurin sa na shirin gyara da ci gaban Borno na tsawon shekaru 25 inda ilimi wani bangare ne da ke samun fifiko.
“Mai girma gwamna ya na sane da wahalhalu da dalibai ke fuskanta, hade da karin kudaden da aka samu a cibiyoyi da dama da kuma fatan tallafin zai taimaka musu wajen biyan kudaden rajista,” in ji Isa.