
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnatin jihar Borno za ta yi kokari ta maida al’ummar da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri zuwa mahallansu cikin mako ɗaya zuwa biyu.
Shettima ya baiyana hakan ne a yayin da ya ke yi wa al’ummar jawabi a Sansanin yan gudun hijira na Bakasi, yayin ziyarar gani-da-ido da ya kai a Maiduguri a jiya Talata.
Ya ce za a yi gaggawar maida al’ummar da ambaliyar ta shafa zuwa mahallansu saboda “ba ma son a sake samun wasu sabbin sansanonin ƴan gudun hijira. Ba abin so ko alfahari ba ne a rika samun sabbin ‘IDP Camps’.”
Bayan ya zagaya guraren da abin ya shafa, Shettima ya tabbatar da cewa gwamnatin taraiya da ta jiha da hukumomin agaji kamar su NEMA, SEMA, NEDC, da RC zasu hada kai wajen tallafawa waɗanda ambaliyar ta shafa cikin gaggawa.
“Ba maganar siyasa, da gaske mu ke za mu tallafa muku cikin gaggawa a kan wannan mawuyacin hali da ku ka tsinci kan ku.
“In Sha Allah gwamnatin jiha, cikin sati daya ko biyu za ta maida kowa mahallinsa.
“Za mu hada kai da hukumomin agaji da gwamnatin jihar Borno wajen kawo muku dauki.
“Mu na yi muku jaje da kuma tausaya wa bisa wannan ibtila’in da Allah Ya aiko mana da shi,” in ji Shettima.