Home Labarai Gwamnatin Buhari ta gina dam 260 a faɗin Nijeriya, in ji Minista

Gwamnatin Buhari ta gina dam 260 a faɗin Nijeriya, in ji Minista

0
Gwamnatin Buhari ta gina dam 260 a faɗin Nijeriya, in ji Minista

Ministan Ruwa da Albarkatu, Suleiman Adamu, ya ce gwamnatin tarayya ta gina madatsun ruwa guda 260 wadanda suka tara ruwa mai faɗin mita biliyan 34 a fadin kasar.

Da ya ke jawabi ga mahalarta taro na 29 na majalisar kula da albarkatun ruwa ta kasa NCWR a jiya Alhamis a Sokoto, Adamu ya ce adadin ya nuna adadin manya da matsakaitan madatsun ruwa da gwamnatin tarayya ta gina.

Ministan ya ce gina madatsun ruwan wani bangare ne na kokarin gwamnati na samar da ruwa na ban-ƙasa da na cikin kasa domin sha, ban ruwa da samar da wutar lantarki.

A cewarsa, Najeriya na da ruwa mai yawan murabba’in mita biliyan 333 da kuma ruwan kasa da ya kai kimanin biliyan 156, wadanda za a iya amfani da su domin biyan bukatar samar da ruwan sha a kasar a halin yanzu.

“Ma’aikata ta na inganta ka’idojin samar da albarkatun ruwa don samar da ruwa isasshen a ƙasar,” in ji shi