Home Labarai Gwamnatin Burkina Faso ta fitar da sabon fasfon tafiye-tafiye ba tare da tambarin ECOWAS ba

Gwamnatin Burkina Faso ta fitar da sabon fasfon tafiye-tafiye ba tare da tambarin ECOWAS ba

0
Gwamnatin Burkina Faso ta fitar da sabon fasfon tafiye-tafiye ba tare da tambarin ECOWAS ba

Gwamnatin soji ta Burkina Faso ta fitar da wani sabon fasfon tafiye-tafiye ba tare da tambarin kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, ba.

Ministan tsaron Burkina Fasfo, Mahamadou Sana ne ya kaddamar da sabon fasfo din.

A tuna cewa Burkina Faso, Nijar da Mali, sun yanke hulda da ECOWAS, sakamakon takunkumin da aka kakaba musu saboda juyin mulkin da sojoji su ka yi.

Da ta ke mayar da martani, ECOWAS ta zargi kasashen uku da nufin tauye ƴancin walwalar yankin.

Sana ya shaida wa manema labarai a wajen kaddamar da fasfo din cewa sauyin ya zo ne ga matakin da Burkina Faso ta dauka na ficewa daga kungiyar ECOWAS, wadda aka yi a watan Janairu.

Ya ce, “A kan wannan fasfo, babu tambarin ECOWAS. Tun daga watan Janairu, Burkina Faso ta yanke shawarar janyewa daga wannan ECOWAS, kuma wannan shi ne kawai fahimtar matakin da Burkina Faso ta riga ta dauka.”