Home Labarai Gwamnatin Jihar Legas za ta ƙara kuɗin kwasar shara da kashi 50

Gwamnatin Jihar Legas za ta ƙara kuɗin kwasar shara da kashi 50

0
Gwamnatin Jihar Legas za ta ƙara kuɗin kwasar shara da kashi 50

 

 

 

Hukumar Kula da Sharar ta Jihar Legas, LAWMA, ta ce ta na duba yiwuwar ƙarin kashi 50 na kuɗin kwasar shara ga kowa da kowa a jihar.

Ibrahim Odumboni, Manajan-Darakta na Hukumar ta LAWMA ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a jiya Laraba a Legas.

Odumboni ya ce an samu karin farashin ne saboda tsadar ayyukan da masu kwasar sharar masu zaman kansu, PSP, ke yi.

A cewarsa, farashin man dizel da ma’aikatan PSP ke amfani da shi ya karu daga Naira 278 a kowace lita a watan Janairu zuwa kusan N875, wanda ya nuna ya karu da kashi 300 cikin 100.

“Muna kan aiwatar da yin nazari mai zurfi game da farashin ayyuka na PSP da ake bayarwa ga gidaje saboda mun san halin matsi da tattalin arziki ya shiga.

“Har ila yau, ba mu gabatar da wani canji da zai gagari masu amfani da kayan mu ba.

“Yayin da farashin mai ya kai kusan kashi 300, muna ba da shawarar karin kashi 50 cikin 100 a fadin hukumar,” in ji Odumboni.