
Gwamnatin jihar Naija za ta haramta sana’ar karuwanci a Minna, a wani bangare na kokarin magance matsalar rashin tsaro a jihar.
Babbar Sakatariya a ma’aikatar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar, Kaltum Rufa’i ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Minna.
Malama Rufa’i ta ce gwamnati ba ta da masaniya kan irin wadannan ayyuka marasa kyau da za su iya kara ruruta wutar kalubalen tsaro da ake fama da shi a jihar.
Ta ce akwai dokokin jihar da suka haramta irin wannan aiki, tana mai cewa gwamnati za ta yi bincike da nufin dakatar da wannan mummunar ɗabi’ar.
“Yanzu da kuka kawo mana maganar, gwamnati za ta fara aiki. Ni da kaina zan je na gana da Sakataren Gwamnatin Jiha don tattaunawa kan lamarin da kuma nemo mafita,” in ji ta.
Binciken da NAN ta gudanar a Minna, ya nuna cewa manyan mata da budurwoyi na fara sana’ar ta su ne daga karfe 7 na dare zuwa tsakar dare a kullum.
Mafi kyawun wuraren da su ka fi tsayawa dojmin an hankalin kwastomomi a Minna sun haɗa da shatale-talen City Gate, sai kuma hanyar Gabas da ke a Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, babban tashar mai, Minna.