
Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da maido da malaman firamare 1,288 da aka kora daga aiki a watan Yunin 2022 bayan kammala jarrabawar tantancewa.
Jami’ar hulda da jama’a ta hukumar kula da ilimin bai daya ta jihar Kaduna SUBEB, Hauwa Mohammed ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Kaduna a yau Laraba.
Hauwa ta bayyana cewa malamai dubu 1,266 ne jarabawar cancantar ta shafa, yayin da wasu 22 kuma aka cire su daga cikin albashin gwamnati bisa zargin su da zama ma’aikatan boge.
Tun a watan Yunin 2022 hukumar ta kori malaman na firamare su dubu 2,357 bayan sun kasa kai manyan su a jarrabawar tantancewa.
Hukumar ta bayyana cewa, daga cikin adadin, an kori malamai 2,192 saboda rashin zana jarabawar, yayin da aka kori malamai 165 saboda rashin kokari a jarrabawar.
Sai dai wasu daga cikin malaman da abin ya shafa, sun koka da cewa sun rubuta jarrabawar sun kuma ci, amma kuma a ka kore su daga aiki, yayin da wasu kuma su ka yi ikirarin cewa ba su da lafiya a lokacin jarabawar tare da bayar da shaida kan hakan.
Don haka kakakin ta shawarci duk malaman da abin ya shafa da su je su karɓi takardun shaidar dawo da su aiki ba daga Sakatarorin Ilimin nasu cikin gaggawa.