Home Labarai Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin raba kayan noma na gwamnatin taraiya a Kano

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin raba kayan noma na gwamnatin taraiya a Kano

0
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin raba kayan noma na gwamnatin taraiya a Kano

Manoma dubu ɗaya ne su ka fara amfana da kayan noma da gwamnatin Kano ta ƙaddamar a ƙarƙashin shirin gwamnatin taraiya mai taken ‘Special Agro-Industrial Processing Zones’, SAPZ.

Shirin na ɗaya daga cikin tsare-tsaren “Sabuwar Rayuwa” na shugaba Bola Tinubu da nufin bunƙasa kimar Nijeriya a matsayin kasuwar duniya, musamman a fannin noma.

Jami’ar yaɗa labarai ta shirin a jihar Kano, Rabi Mustapha, a wata sanarwa da ta fitar ta ce shirin raba kayan noman ya maida hankali a kan noman shinkafa da tumatur a ƙananan hukumomin Bagwai da Kura, inda manoma dubu ɗaya su ka amfana.

A yayin ƙaddamar da shirin, Kwamishinan Noma na jihar Kano, Dakta Danjuma Mahmoud ya yi bayanin cewa gwamnatin Nijeriya da IFAD ne su ka dauki nauyin shirin da nufin bunƙasa noma ta hanyar tallafa wa hazikan manoma da kayan noma.

Ya ja hankalin waɗanda su ka amfana da su tabbata sun yi amfani da kayayyakin da aka ba su don cimma manufar da ake da ita ta bunkasa noma a Nijeriya.