Home Labarai Gwamnatin Kano za ta aiwatar da dokar hana shan shisha a 2022

Gwamnatin Kano za ta aiwatar da dokar hana shan shisha a 2022

0
Gwamnatin Kano za ta aiwatar da dokar hana shan shisha a 2022

 

Gwamnatin Jihar Kano ta ce nan da shekarar 2022 za ta hana shan shisha a fadin jihar.

Babban Daraktan Ma’aikatar yawon Buɗe Ido ta jihar, Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya baiyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Lajawa ya ce wannan wani mataki ne mai kyau wajen daƙile rashin tarbiyya wacce ta kar haifar da aikata munanan aiyuka da za su shafi ƴaƴa masu tasowa.

Babban Daraktan ya baiyana cewa tun 3 ga watan Nuwamba gwamnan Kano ya sanya hannu a dokar wacce za ta fara aiki a shekarar 2022.

“Dokar ta haɗa da masu guraren taro na haya da kuma hana yara ƴan ƙasa da shekara 18 shiga otal.

“Dokar kuma ba ta tsaya a kan hana shan shishar ba, suma masu siyarwar ta shafe su,”

Ya kuma yi kira ga al’umma da su baiwa maikatar haɗin kai domin cimma wannan manufa mai kyau.