
Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta umarci hukumar gudanarwa ta makarantar Kano Capital data janye yi yunƙurin karin kudin makaranta da ta ke yi.
Wannan na ƙunshe a wata sanarwar da Kakakin ma’aikatar, Aliyu Yusuf ya sanya wa hannu a yau Asabar.
Ya ce Babbar Sakatariya a ma’aikatar, Hajiya Lauratu Ado Diso ce ta bayar da wannan umarni yayin da take ƙaddamar da kwamitin da zai yi nazari kan rahotanni kan makarantar na baya da aka gabatarwa ma’aikatar domin aiwatarwa.
Babbar sakatariyar ta tabbatarwa iyayen ɗaliban makarantar cewar ma’aikatar zata tabbatar komin an dora shi kan gurbinsa, ta hanyar amfani da ka’idoji da kuma doka.
Sakatariyar ta kuma bukaci iyayen ɗalibai da su kwantar da hankalinsu sannan kuma su kasance masu bin doka.
Ta kara da cewa an kafa kwamitin ne domin yin nazari kan rahotanni na makarantar da aka gabatar masu game da wasu matsaloli da aka gano domin aiwatar wa da gano hanyoyin gyara.