
Gwamnatin Kano ta fara rushe gine-ginen da aka yi su ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar.
Daily Nigerian Hausa ta kiyo cewa a daren juya Juma’a ne dai gwamnatin ta fara rushe shagunan da aka gina a filin sukuwa, wanda ta ce filayen na gwamnati ne aka sayarwa da wasu tsirari ba bisa ƙa’ida ba.
A tuna cewa a jawabin rantsuwa a ranar Litinin, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya baiwa jami’an tsaro umarnin su mamaye duk wasu gine-gine da aka yi a filayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Gwman yana nufin filayen makarantun, makabartu, badala da sauran filaye mallakar gwamnati, inda ya ce duk gine-ginen da aka yi a nan bayan sayarwa da wasu masu ido da kwalli, sai an rushe su.
Tuni dai aka fara rushe shagunan da aka kammala ginin su kwanan nan a filin sukuwa da ke cikin birnin Kano.
A wani ɓangaren kuma gwamnan ya baiwa masu gine-gine a filin sansanin alhazai da su dakata da gine-ginen.
Ya ce filayen na gwamnati ne kuma an tanadi gurin ne domin sauke alhazai idan za su tafi aikin Hajji, inda ya kara da cewa gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta rushe gine-ginen da aka yi a wajen ta kuma yanka filaye ta sayar.