Home Labarai Gwamnatin Kano ta gano ma’ajiyar gurɓataccen taki da ake sayar wa da manoma

Gwamnatin Kano ta gano ma’ajiyar gurɓataccen taki da ake sayar wa da manoma

0
Gwamnatin Kano ta gano ma’ajiyar gurɓataccen taki da ake sayar wa da manoma

 

 

Gwamnatin jihar Kano ta bankaɗo wata ma’ajiya da aka ajiye gurbataccen taki a Gunduwawa da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa.

Shugaban Hukumar Kare Hakkin mai Saye, CPC, Baffa Babba Dan’agundi, ne ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar, Musbahu Yakasai, yau Laraba a Kano.

“Mun sami bayanan sirri cewa akwai wani mamallakin ma’ajiyar taki yana hada takin da yashi, sanan ya siyarwa manoma.”

“Hakan ya sa muka ɗau matakin rufe ma’ajiyar, domin kare al-ummar jihar Kano daga amfani da taki maras kyau.” Inji shi.

Yakasai ya kuma ƙara da cewa a baya ma hukumar tasu ta kama wata mota a cike da garin semovita mara kyau a kasuwar Singa, inda ya ƙara da cewa hukumar ta kara kama wata ma’ajiyar takin mara kyau a Ƙaramar Hukumar Garko.

Ya kuma nemi al-umma da su cigaba da baiwa hukumar bayanan irin wadan nan gurare domin kare lafiya da ma rayukan al-umma.