
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin gina gidaje kyauta ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce za a yi hakan ne don rage radadin da ambaliyar ta haifar a jihar.
Dawakin Tofa ya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yayin zaman majalisar zartarwa da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a jiya Laraba.
Ya ambato Gwamnan na bayanin cewa gidajen da za a samar za taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa wajen samun matsuguni ga iyalansu.
Ya ce, gwamnatin jihar na hada gwiwa da ma’aikatar jinkai da yaki da talauci domin taimakawa mutanen da kayan abinci da abubuwan rayuwa na yau da kullum.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin raba kujeru da ababen zama a mataki na farko ga daliban makarantun firamare da Sakandare 220, 000 domin inganta fannin koyo da koyarwa.
Gwamna Yusuf, ya ce bisa ayyana dokar tabaci a fannin ilimi a jihar, gwamnatin zata raba kayan makaranta na sawa ga dukkan daliban ajin farko na makarantun firamare.