Home Wasanni Gwamnatin Kano ta gwangwaje ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 47 da naira miliyan 96

Gwamnatin Kano ta gwangwaje ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 47 da naira miliyan 96

0
Gwamnatin Kano ta gwangwaje ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 47 da naira miliyan 96

 

A yau Talata dai, ƴan ƙwallon ƙafar Jihar Kano baki har kunne bayan da gwamnatin jihar ta gwangwaje ƙungiyoyi 47 da kuɗi, wuri na gugar wuri har naira miliyan 96.

Ƙungiyoyin da su ka amfana da wannan tagomashi su ne waɗanda za su fara buga gasannin lig na mataki daban-daban na ƙasa.

Da ya ke jawabi a taron raba kuɗaɗen a gidan gwamnati, gwamna Abdullahi Ganduje ya ce za a rabawa ƙungiyoyin kuɗaɗen ne domin zai taimaka musu wajen fara gasar lig ta ƙasa ta kakar 2021-2022.

Ganduje, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Nasiru Gawuna, ya yi bayani dalla-dalla da cewa ƙungiyoyi 10 da ke gasa mai daraja ta 1 za a bawa kowacce naira miliyan 3, ƙungiyoyi 29 da za su buga gasa mai daraja ta 2 za a baiwa kowacce naira miliyan 2, sai kuma ƙungiyoyi 8 da za su buga gasa mai daraja ta 3, za a baiwa kowacce naira miliyan 1.

“Wannan alƙawari ne da gwamna yai muku kuma ga shi an cika.

“Muna yabawa masu kungiyoyin da su ke ƙoƙarin tafiyar da harkokin kungiyoyin saboda hakan ya sanya matasa sun samu abin yi, maimakon su riƙa aikata aiyukan laifi,” in ji Ganduje.

Daily Nigerian Hausa