
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Bankin Duniya da Hukumar raya Kasar Faransa, sun shirya gina titunan karkara masu adadin tsawon kilomita 6,300 a fadin jihar.
Darakta Janar na Hukumar Raya Karkara da samar da hanyoyi don fito da amfanin gona ta Jihar (RAAMP), Yahaya Adamu Garin Ali ne ya bayyana hakan yayin da yake buɗe horon kwanaki 5 ga mahalarta taron su 152 kan tattara bayanai da dabarun yadda za’a gudanar da aikin a jihar kano.
Sanarwa da jami’in yaɗa labaran shirin a jihar Kano, Adamu Abdullahi ya raba wa manema labarai a yau Laraba a Kano ta ce Garin Ali, ya nanata kudirin Gwamnati na inganta hanyoyin karkara don shiga da fito wa da amfanin gona a jihar.
Don haka DG ya bukaci mahalarta taron da su dauki wannan aiki a matsayin gudunmawar da zasu baiwa jihar Kano, wanda ke bukatar jajircewa da sadaukar da kai don tabbatar da kokarin gwamnatin jihar kanona inganta rayuwar al’ummar jihar nan.
A bangare guda kuma kodinetan aikin na jiha, Injiniya Sunusi Sale Suleiman, ya bayyana horon a matsayin cika sharuddan da bankin duniya ya bukata domin aiwatar da aikin da kuma amfani da manhajar da aka samar do sanya idanu kan yadda ake sarrafa kayayyakin da ake amfani da su a yankunan karkara na Najeriya (NiRTMS) .
Injiniya Suleiman ya kara da cewa, makasudin gudanar da wannan horon shi ne a koya wa mahalasta taron yadda zasu yi amafani da manhajar da aka samar domin bibiyar aiyukan da aka gudanar a yankunan karkara a fadin jihar kano baki daya.