
Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin rushe wani katafaren gini a filin da ke kallon gidan Sheikh Nasiru Kabara da ke cikin birnin jihar.
Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayar da umarnin rusau ɗin, bayan da bincike ya nuna cewa ana yin ginin ne ba tare da izini ba a hukumance.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen hawa ta Kano, KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a yau Talata.
Baffa Babba Dan’agundi, Manajan Darakta na KAROTA, wanda ya zama shugaban kwamitin rushe haramtattun gine-gine ne ya samar da haka a cikin sanarwar.
Sanarwar ta ce da fari, gwamnatin Kano da masarautar su na ta zargin juna kan ko ɗaya da ga cikin su ne ya bada izinin ginin, ya kara da cewa sai da aka gudanar da bincike sai a ka gano ba haka bane.
Sanarwar ta ce yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, Gwamna Ganduje ya bada umarnin katange tare da fitar da wuraren wasanni na yara a filin, yayin da sauran wuraren Kuma yace a bar shi a matsayin Filin da Yan Kadariyya za su yi amfani da shi wajen yin zikiri.
Sanarwar ta ce Ganduje ya kuma bada umarnin a samar da jami’an tsaro isassu domin su tsare yara masu wasa da ma al’ummar yankin baki daya.
A cewar sanarwar, kwamitin ya kuma yi gargadin cewa wadanda ke gudanar da ayyuka ba bisa ka’ida ba a jihar dole ne su daina daga yanzu kamar yadda gwamnati ta kuduri aniyar gurfanar da duk wanda aka kama da laifin karya dokokin jihar game da mallakar filaye da gine-gine.