
Gwamnatin Jihar Katsina ta baiwa iyalin DPO ɗin da ƴan fashin daji su ka kashe, Abdulkadir Rano, tallafin naira miliyan 3.
Rano, wanda Mataimakin Sufritendan Ƴan Sanda, DSP ne, ya rasu tare da wani soja a yayin fafatawa da ƴan fashin daji a Magama da ke Ƙaramar Hukumar Jibiya a ranar Talata.
Kwamishinan Wasanni da Cigaban Al’umma, Alhaji Sani Danlami je ya sanar da bada tallafin ga Kanfanin Daillancin Labarai na ƙasa, NAN a yau asabar a Katsina.
Danlami, wanda ya jagoranci tawogar jami’an gwamnati zuwa ga iyalin marigayin, ya baiyana rasuwar ta sa a matsayin babban rashi ga jihar danƙa rundunar ƴan sanda gaba ɗaya.
Ya ce gwamnatin jihar, a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ta ga irin kokari, jajircewa da sadaukarwar da marigayi Rano ya yi na ganin an kawo zaman lafiya a jihar.
A cewar sa, Marigayin ya sadaukar da rayuwar sa da kuma aiki tuƙuru wajen yaƙi da ƴan fashin daji a yankin Jibiya, inda ya ce hakan ne ya sanya gwamnatin ta ga dacewar kai wa iyalinsa zlzoyara da kuma basu tallafi na gaggawa.