Home Labarai Gwamnatin Kebbi ta ɗaura wa ma’aurata 300 aure

Gwamnatin Kebbi ta ɗaura wa ma’aurata 300 aure

0
Gwamnatin Kebbi ta ɗaura wa ma’aurata 300 aure

Akalla ma’aurata, zawarawa da mara sa ƙarfi yan asalin jiha 300 ne gwamnatin jihar Kebbi ta aurar.

An yi daurin auren, irin sa na farko a jihar a fadar Abdullahi Fodio da ke Masarautar Gwandu a Birnin Kebbi a jiya Lahadi.

Gwamnatin jihar, karkashin Hajiya Nafisa Nasir Idris, uwargidan gwamnan jihar nlce ta shirya daurin auren ƙarƙashin gidauniyar ta mai suna ‘Nafisa Nasir Development Foundation, NANAS’.

Gwamna Nasir Idris, wanda ya jagoranci daurin auren, ya shawarci ma’auratan da su kasance masu nuna so da kauna ga juna.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin kakakin majalisar dokokin jihar, Muhammad Usman Ankwe, ya bayyana cewa gwamnatin za ta ci gaba da gudanar da irin wannan daurin aure lokaci-lokaci don taimakawa marasa karafi maza da mata domin a hada su a matsayin ma’aurata.

Idris ya ce gwamnatinsa ta bayar da Naira miliyan 21 a matsayin sadaki ga amare 300 da suka fito daga kananan hukumomin jihar 21, inda kowacce amarya ta samu sadakin Naira dubu 70.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin ta kuma samar da kayan daki da kayan abinci ga dukkan ma’auratan domin karfafa alakar aurensu.

Ya bayyana cewa an daura auren na jumulla ne bayan tattaunawa da malaman addinin musulunci bisa tsarin koyarwar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wanda ya baiwa mabiyansa izinin yin aure domin amfanin al’umma da kuma samun zuriya masu albarka.