Home Labarai Gwamnatin Kebbi ta bada hutun kwana 2 domin a yi rijistar katin zaɓe

Gwamnatin Kebbi ta bada hutun kwana 2 domin a yi rijistar katin zaɓe

0
Gwamnatin Kebbi ta bada hutun kwana 2 domin a yi rijistar katin zaɓe

 

 

Gwamnatin Jihar Kebbi ta ayyana ranakun Alhamis da Juma’a a matsayin ranakun hutu don baiwa ma’aikatan gwamnati damar samun katin zabe na dindindin, PVC.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Yahaya Sarki, mai baiwa gwamna Atiku Bagudu shawara kan harkokin yaɗa labarai ya fitar a Birnin Kebbi a yau Laraba.

Ya ce matakin zai baiwa ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a damar yi, ko kuma sabunta katin su na PVC don su samu damar nuna ƴancinsu na kada kuri’a.