Home Ƙasashen waje Gwamnatin Kenya ta zabtare farashin masara don sauƙaƙawa talakawa

Gwamnatin Kenya ta zabtare farashin masara don sauƙaƙawa talakawa

0
Gwamnatin Kenya ta zabtare farashin masara don sauƙaƙawa talakawa

 

 

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya bayar da umarnin rage kudin garin masara da sama da rabi domin saukaka wa ‘yan kasar tsadar rayuwa.

BBC Hausa ta tawaito cewa yanzu za a rika sayar da jaka mai nauyin kilogram 2 na garin a kan sulai (shillings) 100, maimakon sulai (shillings) 205 da ake sayarwa a da.

Shugaban ya bayar da umarnin ne bayan wata ganawa da ya yi da ‘yan kasuwa da sauran masu hada-hadar masarar a fadar gwamnatin kasar da ke Nairobi.

Shugaba Kenyatta ya ce daukar matakin ya zama wajibi saboda halin matsi da ‘yan kasar ke ciki sakamakon fari da aka samu da kuma wasu dalilai na waje.

Mista Kenyatta ya caccaki ‘yan siyasa da ya zarga da amfani da tashin farashin garin masarar da yarfen siyasa a yayin da kasar ke tunkarar zabe a ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa.

A sanarwar da fadar gwamnatin ta fitar an dakatar da karbar harajin tashar jirgin kasa da kuma kudin fito na shigar da masara kasar ta gabashin Afirka.