
Yayin da a ke ci gaba da dawo wa harkokin karatu a jami’o’in kasar nan ke bayan yajin aikin ASUU na tsawon watanni 8, akalla dalibai 900 ne ‘yan asalin jihar Kwara a ka kwashe su zuwa jihohi 13 ciki har da babban birnin tarayya.
Daliban da aka yi jigilar su kyauta an yi kai su zuwa makarantunsu a cikin motocin bas-bas masu cin mutum 18 kusan guda 50 a ranakun Asabar da Lahadi.
Gwamnatin ta ce matakin na nuni ne da yadda ta damu da halin da daliban ke ciki.
Wata sanarwa da jami’iar yada labarai na ma’aikatar ilimi ta jihar, Mansurat Amuda-kannike, ta fitar ta ce “Kwamishinan ilimin manyan makarantu, Dakta Alabi Afees Abolore, ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ta yanke shawarar bayar da sufuri kyauta ga daliban Kwara da ke karatu a Arewa, domin samun sauki ga iyayensu bayan dakatar da yajin aikin ASUU.
“Idan za a iya tunawa, ma’aikatar ta sanar da shirin zirga-zirgar ababen hawa kyauta ne kwanaki kadan da suka gabata, a wani yunkuri na taimaka wa daliban da suka dawo yankin Arewacin kasar nan.