
Gwamnatin Jihar Legas ta ce tana bincike kan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta, inda wasu ke raba man fetur a cikin jarakuna a matsayin kyautar halartar biki.
Kwamashinan Yaɗa Labarai na Legas, Gbenga Omotoso, ya ce “shakka babu wannan lamarin abin haɗari ne kuma zai iya jawo rasa rayuka da dukiyoyi”.
A jiya Asabar fefen bidiyon ya ɓulla, inda aka ga jarakunan fetur masu lita 10 a jere da za a raba wa mahalarta bikin.
Jaridar Daily Trust ta ce Chidinma Pearl Ogbulu ce ta shirya taron don murnar naɗa ta a matsayin Erelu Okin.
Yanzu haka ƴan Nijeriya na fama da ƙarancin man fetur, inda suke shafe awanni masu yawa a kan dogayen layuka a gidajen mai kafin su samu.