
Gwamnatin Naija ta hana haƙar ma’adanai
Gwamnan Jihar Naija, Abubakar Sani Bello, ya sanya dokar dakatar da haƙar ma’adinai a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da kuma Rafi.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Malam Ahmed Ibrahim Matane ya fitar da yammacin yau Litinin.
Ta cikin sanarwar ‘, sakataren ya ce akwai buƙatar a dakatar da haƙar ma’adinai sakamakon yadda rashin tsaro ke ƙara ƙamari ƴan kwanakin nan ta yadda ƴan bindiga ke kai hare-hare.
Haka kuma ya ƙara da cewa an lura da cewa wuraren haƙar ma’adinai na janyo masu aikata laifuka waɗanda ke ci gaba da zama barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamnatin jihar ta Neja, ta kuma yi gargaɗin cewa duk mutanen da aka kama suna haƙar ma’adinai a yankunan da aka sanya dokar za su fuskanci hukunci.