
Gwamnatin Jihar Naija ta hana sayar da babura a faɗin jihar.
Sakataren Gwamnati, Ahmed Ibrahim Matane ne ya sanar da dokar a wata sanarwa a yau Asabar.
Matana ya ce hana sayar da baburan ya faru ne sakamakon rashin tsaro a wasu ɓangarori na jihar, inda ƴan ta’adda ke neman a basu babur a matsayin kuɗin fansa.
“Gwamnan Jihar Naija, Abubakar Sani Bello ya bada umarnin hana sai da babura a jihar nan da gaggawa,” in ji sanarwar.
Baburan da a ka hana sun haɗa da Bajaj, Boxer, Qiujeng, Honda ACE, Jingchen, da sauran su.