Home Kanun Labarai Gwamnatin Najeriya ta yi karin bayanin yadda zata kashe dala biliyin daya don yaki da Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta yi karin bayanin yadda zata kashe dala biliyin daya don yaki da Boko Haram

0
Gwamnatin Najeriya ta yi karin bayanin yadda zata kashe dala biliyin daya don yaki da Boko Haram

Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta bayyana masu kalubalantar shirinta na kashe dalar Amurka biliyan daya domin yaki da Boko Haram da sauran yayukan ‘yan ta’adda da cewar, sam mutane basu fahimci abin ba, kuma basu yi mata uzuri ba, suke yin kalamai na suka a gareta, a cewar Gwamnatin wannan sam bai dace ba kuma abin kunya ne.

Kakakin Gwamnatin Najeriya kuma ministan watsa labarai da raya al’adu na kasa Alhaji Lai Mohammed ne ya tattauna hakan da  manema labarai a Legas.

Yace, asali Gwamnonin Najeriya sun yi abinda ya dace, wajen sahalewa gwamnatin tarayyar najeriya, domin ta tsakuri wani abu daga asusun ajiyarta na ko ta kwana, domin yaki da ayyukan ‘yan ta’adda.

Alhaji Lai Mohammed ya kara da cewar, ba wai an ware dala biliyan daya bane kawai da a yaki Boko Haram a Arewa maso gabas, yace ba haka bane, wannan makudan kudi da su za a yaki sauran ayyukan ta’addanci a najeriya, kamar Satar mutane da yin garkuwa da su, da kuma sauran ayyukan tsageru.

Yace abin ya bashi mamaki, aikin da Gwamnati take son yi domin walwalar ‘yan Najeriya, amma wasu sun yi masa gurguwar fahimta da gangan.

Lai yace, abinda mutane basu sani ba shi ne, makaman da ake yaki da Boko Haram da su, masu dan karen tsada ne, dan haka dole ne mu nemo su domin kai karshen wannan yaki.

Na fada na kuma nanatawa, ba daidai bane, mutane su mayar da al’amarin tsaron kasa ya zama siyasa, muna da sojojinmu da suka sadaukar da rayuwarsu domin wannan kasar, to, bai kamata mu shigar da siyasa cikin komai ba musamman batun tsaro.

“Masu adawa da kashe wannan kudi dala biliyan dayaa, sam basu kyauta ba, domin sun sanya siyasa cikin lamarin sosai, sun manta kungiyar Gwamnonin Najeriya ce ta zauna, ta sahalewa Shugaban kasa amfani da wannan kudin domin yaki da Boko Haram da sauran ayyukan ‘yan ta’adda”

“Jami’an tsaron Najeriya suna taka muhimmiyar rawa domin yaki da ayyukan ta’addanci ba wai Boko Haram kadai ba, dan haka dole mu tallafawa wannan kokari nasu da kayan aiki sabbi kuma na zamani”

“Dan mun karya lagon ‘yan Boko Haram, ba shi ne yake tabbatar mana da cewar mun zo karshen yaki da su ba, sanin kowa ne, yaki da ‘yan sari ka noke ba daidai yake da yaki na gaba da gaba ba”

“Mafiya yawancin masu adawa da kashe wannan dala biliyan dayar, galibinsu suna tunanin an gama da Boko Haram ne, basu san cewar an kashe maciji ne ba’a sare kansa ba”

“Mutane basu sani ba cewar irin wannan yaki da muke yi da ‘yan BokoHaram yafi ko wane yaki cin kudi da wahalarwaba, domin shi ba kamar yaki bane da aka sani, wasu makaman da za’a saya masu masifar tsada ne da kuma wuyar samu”