Home Labarai Gwamnatin Nijeriya za ta yi ƙarin albashi

Gwamnatin Nijeriya za ta yi ƙarin albashi

0
Gwamnatin Nijeriya za ta yi ƙarin albashi

 

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta yi ƙari a kan albashin ma’aikata domin rage raɗaɗin.agsalsr tattalin arziki a kasar nan.

Chris Ngige, Ministan Kwadago da Aiki ne ya bayyana haka a wajen taron ƙaddamar da mujallu 40 na kungiyar ƴan kwadago, NLC, a jiya Litinin a Abuja.

Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya ta na da masaniyar cewa darajar mafi karancin albashi na Naira 30,000 ta ragu.

“Eh hauhawar farashin ya karu a duniya kuma bai takaita a Najeriya ba, shi ya sa a yawancin ɓangarori an yi gyara ne na ma’aikata a yanzu.

“Mu a matsayinmu na gwamnatin Najeriya, za mu yi ƙari domin yayi daidai da yanayi tattalin arziki.

“Dokar mafi karancin albashi ta kasa na 2019, a yanzu tana da sharaɗi na sabunta ta, wanda muka fara a lokacin, ban sani ba ko shekara mai zuwa ne ko kuma 2024.

“Amma kafin wannan lokacin, gyaran albashin zai kasance ne da duba kan yanayin tattalin arziki, kamar yadda gwamnati ta fara daidaitawa da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU),” inji shi.