
A yau Talata ne gwamnatin tarayya ta gabatar da takardar shaidar yin rijista ga sabbin kungiypyon malaman jami’a, Congress of Nigerian Academics Academy, CONUA, da National Association of Medical and Dental Academic, NAMDA.
Chris Ngige, Ministan Kwadago da Aiki ne ya gabatar da takardun shaida ga kungiyoyin a wani taro a Abuja.
“An amince da kungiyoyi biyu a hukumance kuma an yi musu rijista don a rusa kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da kuma kungiyar likitoci ta kasa (NARD),” in ji Ngige.
Ya ce an yi wa kungiyoyi biyun dokoki a hukumance, don haka su na da hakki na ma’aikata kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya da kungiyar kwadago ta kasa da kasa, ILO, ta tanada.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na tsara hanyoyin biyan albashin ma’aikatan CONUA da NAMDA na tsawon yajin aikin da ASUU ta yi.
Ministan ya kara da cewa zai zama rashin adalci idan aka yi musu hukumci domin tun farko ba su taba shiga yajin aiki ba.
Ngige ya kuma bayyana cewa, rashin bin tsarin dimokuradiyya, gaskiya da kuma rashin biyan kuɗin ƙungiya da ya dace da ASUU ke yi, ga mambobinta da gwamnati ya kai ga ƙirƙirar sabbin kungiyoyin nan.