
Gwamnatin tarayya ta yi barazanar daukar ma’aikatan wucin-gadi ta riƙa biyan su da albashin ma’aikatan da ke yajin aikin.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ne ya bayyana hakan a wani shirin gidan talabijin na Channels.
Kungiyar Likitocin Al’umma ta Ƙasa (NARD) ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyar, a jiya Laraba, saboda rashin biyan bukatunsu.
Kungiyar ta kuma bukaci a kara wa tsarin albashin likitocin da ya kai kashi 200 cikin 100 na albashin da likitoci ke karba a halin yanzu; sabbin alawus-alawus da ke kunshe a cikin wasikar ta zuwa ga Ministan Lafiya a ranar 7 ga Yuli, 2022, kan batun tsarin albashi na CONMESS; biyan su kuɗin horon aikin likitanci na 2023; biyan bashin albashi da kuma daidaita sakamakon mafi karancin albashi.
Sai dai kuma Ngige ya ce likitocin ƙorafin ƙarya su ke yi.
Ya kuma ce NARD ta raina kungiyar likitocin Najeriya (NMA), wadda tuni ta fara tattaunawa da gwamnati a madadinta.
“Likitocin su ma ɓangare ne na NMA. Su matasan likitoci ne da ke ɗaukar horo. Don haka idan har NMA suna tattaunawa a madadinsu a matsayinsu na uwar kungiya, abin da wadannan matasa (likitoci) suke yi shi ne rashin mutunta NMA. Ba su da dalilin ƙorafi,” inji shi.