Home Labarai Gwamnatin Nijeriya ta nemi iyayen ɗalibai da su roƙi ASUU ta janye yajin aiki

Gwamnatin Nijeriya ta nemi iyayen ɗalibai da su roƙi ASUU ta janye yajin aiki

0
Gwamnatin Nijeriya ta nemi iyayen ɗalibai da su roƙi ASUU ta janye yajin aiki

 

Gwamnatin Najeriya ta nemi iyayen ɗalibai a ƙasar da su roƙi malaman jami’a su jingine yajin aikin da suke yi tsawon wata biyar “saboda ta yi abin da za ta iya”.

Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels a yammacin Juma’a.

Ministan ya ce tun kafin ƙungiyar malaman ta ASUU ta fara yajin aikin gwamnati ta kira su don tattaunawa amma duk da haka sai da suka tafi yajin aikin.

Da aka tambaye shi ko me zai faɗa wa iyayen da yaransu ke ci gaba da zaman gida har yanzu, sai ya ce: “Zan ce musu su je su roƙe su [ASUU]. Kamar yadda shugaban ƙasa ya faɗa a baya, waɗanda suka san su su roƙe su don nuna kishinsu ga ƙasar.”

Ya ci gaba da cewa: “…Me za mu yi fiye da haka? Tun kafin a fara yajin aikin muka kira su. Ba wai ƙyale su muka yi ba kawai muka kama barci. Ba zai yiwu ka ƙyale mutum ya ci kwalarka ba kuma ya tilasta maka ciyo bashin naira tiriliyan ɗaya.”

A farkon makon nan ne ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da mako huɗu, ƙari a kan wata biyar da ta shafe bayan jingine aiki a jami’o’in Najeriya