
Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Clem Agba, a yau Juma’a ya kaddamar da ɗakin kula da yanayi da bayanan talauci na kasa, PDSR.
Agba ya kaddamar da PDSR ɗin ne ƙarƙashin Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Ya ce cibiyar ta za ta gabatar da ingantaccen tsari na fahimtar yanayin talauci a Nijeriya.
Ministan ya ce manufar ita ce a samu cibiyar tattara bayanai na talauci da kuma walwalar jama’a tare da fasali daban-daban inda za a riƙa zama a tattauna wasu manufofi da za a ƙirƙiro da su a kan yanayin.
Agba ya ce cibiyar ta bayanai za ta ba da dama ga jama’a don samun ƙarin ilimi da fahimtar ra’ayoyi da hanyoyin yadda ake yin ma’aunin talauci da kuma yadda za a iya amfani da bayanan a aikace.