
Gwamnatin Taraiya ta sanar da Litinin, 27 ga watan Disamba, Talata, 28, ga Disamba, 2021 da kuma Litinin, 3 ga watan Janairu, 2022 a matsayin ranakun hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya yi sanarwar ta hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Dakta Shuaib Belgore a yau Laraba da safe.
“Dole ne mu yi koyi da rayuwar Yesu Almasihu ta ɓangaren yadda ya ke aikata wa da koyi da kyawawan halaye, hidima ga al’umma, tausayin alumma, haƙuri, son zaman lafiya da kuma kyawawan halaye da ya nuna su bayan haihuwarsa.
“Wannan itace hanya mafi inganci ta yin murna da haihuwar Yesu Almasihu,” in ji wani ɓangare na sanarwar.
A duk faɗin duniya a na bikin Kirsimeti ne a ranar 25 ga watan Disamba.
Ita kuma sabuwar shekara, a na yin hutun shigowar ta ne a ranar 1 ga watan Janairu.