
Gwamnatin taraiya ta sanar da cewa ƴan ƙasa za su hau jirgin ƙasa kyauta daga 24 ga watan Disambar da mu ke ciki zuwa 4 ga Janairu, 2022.
Manajan Darakta na Hukumar Kula da Harkokin Jirgin Ƙasa, Fidet Okhiria ne ya baiyana hakan a wata ganawa da ya yi da Kanfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Juma’a a Abuja.
Ya cean ɗauki matakin ne domin saukakawa ƴan ƙasa su yi zirga-zirga a lokutan bikin Kirsimeti.
“Mu na kira ga fasinjoji da su je su karɓi sahihin tikiti a guraren da su ka dace.
“Mu na kira ga fasinjoji da su bi ƙa’idojin kariya da ga kamuwa da korona ta hanyar sanya takunkumin fuska,” in ji shi.