
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta sayi motocin da kudinsu ya kai Naira biliyan 1 da miliyan dari 4 domin taimakawa jamhuriyar Nijar wajen magance matsalar rashin tsaro.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare ta Kasa, Zainab Ahmed, ce ta tabbatar da hakan a jiya Laraba, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya.
Ta ce shiga lamuran makwabciyarta Jamhuriyar Nijar ba sabon abu ba ne, kuma hakkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da sayen.
Ta kara da cewa tallafin na kudi wanda aka fi mayar da shi don inganta tsaro a yankunansu, bisa bukatar gwamnatin Nijar shi ma yana da amfani ga kasar.
Ministar ta bayyana hakan ne yayin da take amsa tambayoyi dangane da wasu takardu da aka fitar a shafukan sada zumunta wadanda suka nuna cewa shugaban kasar ya amince da fitar da kudaden a ranar 22 ga watan Fabrairun Shekarar 2022 ga Jamhuriyar Nijar.