
Najeriya na shirin kara yawan daliban makarantun firamare daga kashi 46 na yanzu zuwa kashi 90 cikin 100 a wannan shekara ta 2030.
Haka kuma kasar na shirin rubanya yawan mata a makarantu tare da tabbatar da kammala karatun sakandare daga kashi 42 zuwa kashi 80 nan da shekarar 2030.
Yosola Akinbi, Ko’odinetan Hukumar Bunƙasa Rayuwar Dan’adam ta Kasa, HCD, karkashin kwamitin Tattalin Arziki na Kasa ne ta bayyana hakan a Benin.
Da ta ke jawabi a wajen bude taron na kwanaki biyu na yankin Kudu-maso-Kudu kan bunkasa ratuwar dan’dam, Akinbi ta ce an sanya aikin ne domin inganta tsarin ilimi mai hade da aiki.
Ta kuma ce a shirye ta ke don inganta daidaito wajen saukaka kiwon lafiya da inganci ga kowane dan Najeriya.
“Muna kuma duban rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta da kashi 70 cikin 100,” in ji ta.
Misis Akinbi ta lura da cewa taron da aka gudanar don jawo hankalin gwamnatocin jihohi don tabbatar da ba da fifikon saka hannun jarin a kan bunkasa rayuwar dan’dam.
Ta ce aikin ya mayar da hankali ne kan batutuwa uku da suka shafi kiwon lafiya da abinci mai gina jiki, ilimi da shigar da ma’aikata.