Home Labarai Gwamnatin Nijeriya na shirin hana cin ganda a faɗin ƙasar

Gwamnatin Nijeriya na shirin hana cin ganda a faɗin ƙasar

0
Gwamnatin Nijeriya na shirin hana cin ganda a faɗin ƙasar

 

 

 

 

 

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa tna nan ta na shirin yin wata doka da za ta hana cin ganda a faɗin ƙasar.

Darakta Janar na Cibiyar Fasahar Kimiyya da Sarrafa Fatun Dabbobi, NILEST, Muhammad Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce dokar ta zamo dole domin a farfaɗo da harkar sarrafa fata a faɗin ƙasar nan.

Ya ce za a yi dokar ne domin farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata a ƙasar nan.

A cewar sa, dole ne gwamnati ta hana cin ganda, wacce ba ta da wani amfani wajen gina jikin ɗa’adam.

Ya ƙara da cewa hana cin gandar da farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata zai bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce akwai lokacin ma da a ka taɓa tura ƙudurin a majalisa kuma an tattauna a kansa amma ban san ya a kai a ka ajiye shi ba.

“Idan a ka tabbatar da dokar a majalisa, to tabbas za ta farfaɗo da kamfanunuwan sarrafa fata a ƙasar nan,” in ji shi.