
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa an fitar da naira biliyan 1.2 ne domin gina sabbin rijiyoyin burtsatse ba gyara su ba.
A tuna cewa, a kwanan nan Gwamna Ahmad Aliyu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kashe Naira biliyan 1.2 wajen gyaran rijiyoyin burtsatse guda 25 a wasu kauyuka biyar na jihar.
Rahoton ya janyo suka mai yawan gaske, inda da dama suka yi ta korafi cewa adadin ya yi yawa a ce an kashe wannan makudan kuɗaɗen wajen gyaran rijiyoyin burtsatse.
Sai dai da ya ke jawabi a taron manema labarai, kwamishinan muhalli na jihar, Nura Shehu, ya ce rijiyoyin burtsatse da gwamnan ya yi magana da akai, sabbi ne da aka gina tare da tallafin bankin duniya.
Ya bayyana cewa ƙauyukan ba su da rijiyoyin burtsatse da kuma samun ruwa mai inganci kafin zuwan gwamnati mai ci.
A cewarsa, sabbin rijiyoyin burtsatse da aka haƙa na cikin yankuna biyar daban-daban da suka haɗa da Munki, Manuna, Lugu, Kinawa, da Dawuru.
Ya yi nuni da cewa ana gudanar da irin wadannan ayyuka a fadin Arewacin Najeriya, da suka hada da jihohin Kebbi, Zamfara, da Katsina.