Home Labarai Gwamnatin Taraiya ta ƙaddamar da matatar mai da za ta riƙa tace ganga 10,000 a rana a Edo

Gwamnatin Taraiya ta ƙaddamar da matatar mai da za ta riƙa tace ganga 10,000 a rana a Edo

0
Gwamnatin Taraiya ta ƙaddamar da matatar mai da za ta riƙa tace ganga 10,000 a rana a Edo

 

 

 

A yau Alhamis ne Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da matatar mai ta kamfanin Duport Midstream Energy Park a unguwar Ogbekor, Ƙaramar Hukumar Orhionmwon a jihar Edo.

Matatar za ta kasance za a rika tace ganga 10,000 a kowace rana, inda a ke sa ran za ta fara tace gangar mai 2,500 a ranar da ga ranar 28 ga watan Yuli.

Da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala rangadin ginin matatar, Simbi Wabote, Babban Sakataren Hukumar Bunƙasa wa da sa ido a kan kayayyakin da ke samarwa na cikin gida, NCDMB, ya ce matatar ta kasance ta biyu da za a buɗe a watan Yuli.

“A halin yanzu, ɗaya daga cikin matatun man namu ta na aiki, wanda shine Watersmith modular matatar mai da ke tace ganga 5,000 a rana da za ta rika samar da mai ga kasuwar Gabashin ƙasar nan

“Game da aikin matatun mai na zamani, nan da watan Yuli, wannan zai ci gaba da nuna muku cewa akwai matatun mai da ke aiki a kasar nan.

“Muna godiya ga abokan huldarmu, NNPC da kuma Seplat da suke samar mana da danyen man da ake so. A nan, muna aiki tuƙuru tare da kamfanin mai na summit mai da sauran abokan hulɗa da ke son haɗa gwiwa da mu don samar da danyen mai.

“Tsarin shi ne a ranar 18 ga watan Yuli, DPR za ta zo ta yi bincike na karshe game da ba mu izinin shigar da iskar gas a cikin matatar.

“Don haka, daga yanzu zuwa karshen watan Yuli, wannan matatar man ban da wadda muke da ita a Ibigwe, za ta fara aiki.”