Home Ilimi Gwamnatin Taraiya da ASUU za su dawo zaman sulhu a mako mai zuwa

Gwamnatin Taraiya da ASUU za su dawo zaman sulhu a mako mai zuwa

0
Gwamnatin Taraiya da ASUU za su dawo zaman sulhu a mako mai zuwa

 

 

 

 

Gwamnatin Taraiya ta bayyana cewa a mako mai zuwa za ta dawo teburin sulhu da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU a kan kawo ƙarshen yajin aikin da su ke yi.

Ministan Ƙwadago da Samar da Aiki, Chris Ngige ne ya bayyana hakan a jawabin buɗe taro a wani taro tsakanin gwamnatin da kuma Ƙungiyar Malaman Ilimin Fasaha, NAAT.

A cewar Ngige, za a iya kawo ƙarshen rikice-rikicen yajin aikin kungiyoyi a ɓangaren ilimi,nisan da kungiyoyin sun yi riƙo da irin tsare-tsaren da ya fito da su kamar yadda ƙungiyoyin fannin lafiya su ka yi riko da su.

Ya ce irin tsare-tsaren na da ya ɓullo da su a buɗe shine ya janyo a ka samu zaman lafiya da ƙungiyoyin ma’aikata na fannin lafiya.

Sai dai kuma ministan ya koka a kan irin takara da ke tsakanin kungiyoyin biyu na fannin ilimi, inda ya fayyace musu cewa kowacce ƙungiya na da muhimmanci a tsarin karatun jami’a.

Ngige ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatin na iya bakin ƙoƙarin ta na daƙile rikice-rikicen da ke fannin lafiya gaba dayan sa, inda ya ce gwamnati na da cikakkiyar masaniyar cewa babu wata ƙungiya da za ta samu nasara ba tare da ƴar uwar ta ba.