
Gwamnatin tarayya ta mika motocin bas guda 64 masu amfani da gas (CNG) ga wakilan kungiyoyin kwadago da suka hada da TUC, NLC, da kungiyar dalibai ta kasa NANS.
An gudanar da mika motocin bas din ne a jiya Lahadi a babban dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, a wani bangare na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
Wale Edun, Ƙaramin Ministan Tattalin Arziki na Kasa kuma Ministan Kudi ne ya jagoranci tawagar gwamnati wajen bikin mika motocin.
Edun ya ce idan aka fara amfani da motocin bas din za su rage tsadar zirga-zirgar ababen hawa a kasar, wanda hakan zai sa a samu ingantaccen tsarin motocin haya da araha.
Comrade Nuhu Toro, Babban Sakatare kuma Shugaban Hukumar TUC; Comrade Lucky Emonefe, shugaban NANS, da Comrade Uche Ekwe, shugaban sashin kula da harkokin kasa da kasa, NLC, sun yabawa Tinubu kan wannan karimcin.
Sun yi kira da a samar da karin motocin bas din masu amfani da CNG ga jama’a.
Mista Toro ya godewa shugaban kasa kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 na kasa.