
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya za ta kafa wani kwamiti da zai dubo tare da shawo kan matsalar wutar lantarki a wasu sassan Nijeriya.
Adelabu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na X bayan wani taro da kamfanonin rarraba wutar lantarki da samar da wutar lantarki a yau Juma’a a Abuja.
“Na yanke shawarar kafa kwamitin da ya shafi dukkan masu ruwa da tsaki. Tare, za mu yi aiki kan shawarwari don warware waɗannan batutuwa tare da tabbatar da samar da wadatacciyar wutar lantarki ga ‘yan ƙasa.
A jiya, na yi tattaunawa mai mahimmanci da Kamfanonin samar da Wutar Lantarki (GenCos) da Kamfanonin Rarraba wutar lantarki (DisCos) don magance matsalar rashin wutar lantarki da ke faruwa a sassan kasarmu.
“wutar lantarki ta samu a lokacin bukukuwan Kirsimeti, amma abin takaici sai ake fuskantar koma baya a sabuwar shekara.
“Bayan bincike, a bayyane yake cewa babban dalilin rashin wutar lantarki shine karancin iskar gas ga GenCos,” in ji shi.