
Gwamnatin Najeriya ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su hana masu amfani da layukan waya yin kira da layukansu idan har ba su yi rajista sun kuma haɗa su da lambar zama ɗan kasa ba (NIN) da ga yau Litinin.
Hukumar kula da Harkokin Sadarwa ta Ƙasa, NCC tare da Hukumar kula da yin Rijistar ƴan Ƙasa (NIMC) ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da su ka fitar.
Wannan matakin na nufin wadanda aka rufe layukansu saboda rashin hada su da lambar dan kasa ba za su iya kiran kowa ba, sai dai za a iya kiransu.
Ministan Sadarwa na Ƙasa, Isa Ali Pantami ne ya bayar da umarnin.
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce kawo yanzu, ta mika lambobin waya miliyan 125 domin a hada su lambar dan kasa, kuma hukumar NIMC ta yi rajistar lambobin dan kasa miliyan 78 kawo yanzu.
Sanarwar ta ce “Muna ba dukkan wadanda aka dode layukansu daga yin waya, da su tafi cibiyoyin da ake yin rajista domin hada lambobin nasu da lambar dan kasa domin kamfanonin sadarwa su iya bude musu layukan nasu.