
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da karɓar kashi 5 na haraji da ga katin kiran waya, jaridar The Cable ce ta gano hakan.
Jaridar ta gano cewa harajin na ɗaya daga cikin sabbin haraje-haraje da a ka ɓullo da su a dokar kuɗaɗe ta ƙasa ta 2020 da Buhari ya rattaba hannu.
A sanarwar da The Cable ta gani, Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta baiwa Hukumar Kwastan umarnin fito da wani tsari na cajar harajin a kan katin kiran waya, mitar wutar lantarki da sauran su a kan kashi 5 cikin 100.
The Cable ta kuma gano cewa gwamnatin taraiya na shirin tara a ƙalla Naira Biliyan 150 da ga harajin, inda za ta baiwa Hukumar Kwastan na’ura biliyan 10 a ciki, daidai da kashi 7 na kuɗin, a matsayin ladan karɓar harajin da ga hannun ƴan ƙasa.
Katin waya na ɗaya da ga cikin kayayyakin da a ka saka za a riƙa karɓar haraji na kashi 5, wanda a ke shigo wa da su ko kuma a nan cikin gida a ke ƙera su, shine sai a saka musu haraji a lokacin da a ke ƙera su, kamar yadda sashi na 21(1) na dokar ya tanada.