Home Labarai Gwamnatin Tarayya ce ta ƙagi talauci a Nijeriya ba mu ba, Gwamnoni sun maida martani

Gwamnatin Tarayya ce ta ƙagi talauci a Nijeriya ba mu ba, Gwamnoni sun maida martani

0
Gwamnatin Tarayya ce ta ƙagi talauci a Nijeriya ba mu ba, Gwamnoni sun maida martani

Kungiyar gwamnonin jihohi ta Najeriya ta ce ikirarin da gwamnatin tarayya ta yi a kan cewa gwamnonin jihohin kasar su ne suke da alhakin karuwar talauci a kasar, magana ce da ba ta da tushe ballantana makama.

Kungiyar ta NGF ta mayar da martani ne kan kalaman da karamin ministan kudi na kasar Clem Agba ya yi a baya-bayam nan inda ya zargi gwamnonin da rashin daukar matakan inganta rayuwar mazauna karkara.

A maimakon haka ya ce sun fi ba ayyukan samar da ababan more rayuwa a birane fifiko da yin gine-gine.

A cewar ministan kudin kashi 72 cikin 100 na al’ummar kasar da ke fama kangin talauci na zaune ne a yankunan karkara inda ya yi ikirarin cewa gwamnoni sun yi watsi da su.

Sai dai Abdul Razak Bello Barkindo wanda shi ne kakakin kungiyar gwamnonin ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa kalaman ministan ya bai wa gwamnonin kasar mamaki.

“ Ba mu zaci cewa shi wannan ministan zai yi furuci irin wannan ba, dalili kuwa shi ne ba mu saba ka-ce-na-ce da gwamnatin tarayya ba, sannan kuma bai cancanta ba, saboda gwamnatin tarayya tana da gwamnoni 22 a cikin jam’iyyarta.’’ In ji shi.

Ya kara da cewa, ‘’Idan gwamnatin tarayya tana ganin akwai abin da ya kasa toh ina ganin irin manufofin jam’iyyar ce ta kasa., ba su hana su yi abin da ya kamata su yi ba.’’

Sai dai karamin ministan kudin a bayaninsa ya yi karin haske a kan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka don yaki da talauci a kasar inda kuma ya zargi gwamnonin da aiwatar da ayuykan da ba za su yi tasiri ba wajen inganta rayuwar talaka.

A dayan bangaren kuwa kungiyar gwamnonin jihohin Najeriyar ta ce gazawar gwamnatin tarayya ce ta janyo karuwar talauci a cikin kasar kamar yadda kakakinta ya bayyana:

‘’ Ai gwamnatin tarayya ita take da hakkin tabbatar da cewa karkarar Najeriya tana da tsaro, sannan manoma suna iya zuwa gonakinsu, sannan ‘yan kasuwa na iya zuwa kasuwanci, sannan ‘yan makaranta na iya zuwa makaranta domin in babu tsaro ba yadda za a yi a samu zaman lafiya a kasar” in ji shi.

Bello-Barkindo ya kara da cewa ba dai dai ba ne gwamnatin tarayya ta tsame hannunta daga talaucin da ya yi katutu a kasar yayin da rahotanni ke nuna cewa ‘yan Najeriya miliyan 130 na cikin kangin talauci.

A jawabin da karamin ministan ya yi wa manema labarai bayan da aka kammala taron majalisar ministoci a ranar Laraba, Mista Agba ya bayyana jihar Sokoto a matsayin jihar da aka fi samun yawan mutanen da ke fama da bakin talauci, sai kuma jihar Bayelsa da ke binta a baya.

Sai dai ministan ya ce abin dubawa a nan shi ne cewa ba maganar rashin kudi ba ne matsalar saboda jihar Bayelsa na da arzikin man fetur, a don haka matsalace da ta shafi yadda ake kashe kudi wajen aiwatar da wasu ayyukan wadanda ba sa tasiri wajen inganta rayuwar talaka.