Home Labarai Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Naira Biliyan 2.6 domin tsaron Abuja

Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Naira Biliyan 2.6 domin tsaron Abuja

0
Gwamnatin tarayya ta amince da kashe Naira Biliyan 2.6 domin tsaron Abuja

 

Majalisar Zartaswa ta Tarayya, FEC, ta amince da Naira biliyan 2.6 don siyan motoci da na’urori ga jami’an tsaro da ke aiki a babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Muhammed Bello ne ya bayyana haka a lokacin da suke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa kan sakamakon taron majalisar na yau Laraba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron na yau Laraba a Abuja.

Bello ya bayyana cewa majalisar ta amince da Naira biliyan 2.6 don siyan motocin aiki da na’urori ga hukumomin tsaro domin yaƙar aikata laifuka a ɗaukacin Kananan Hukumomi shida na babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce: “A yau, na gabatar da ƙudirin sayan motocin aiki, na’urorin tsaro da na’urorin da za su tallafa wa jami’an tsaro da ke aiki a babban birnin tarayya.

“Wadannan kayayyaki motocin amfani ne guda 60 da suka hada da na’urorin sadarwa da za a saka a cikin motocin, wadanda za a kawo su a kan kudi N1,835,108,613,.95 tare da kawo su nan da watanni biyu.”

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin FCT ta kuma samu amincewar sayo karin kayayyakin aiki ga hukumomin tsaro da ke da alhakin tabbatar da tsaro a yankin.