
Gwamnatin tarayya, a Litinin, ta bayyana cewa farashin takin na ci gaba da hauhawa ne sakamakon karuwar kayayyakin da ake haɗa takin a duniya.
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a Abuja a taron nuna ayyukan da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi, karo na biyar.
Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu ce ta shirya jerin tarukan, inda karo na biyar ya karɓi bakuncin Ministan Noma da Raya Karkara, Dakta Mohammad Abubakar.
Da ya ke amsa tambaya kan tsadar taki a kasar, ministan yada labarai da al’adu ya ce lamarin ya shafi duniya baki daya.
Ya bayyana cewa daga shekarar 2017 zuwa yau, farashin manyan kayan da ake haɗa taki guda uku, wato phosphate, potash da urea, ya yi sama sosai.
“A shekarar 2017, tan daya na phosphate ya kai Dalar Amurka 290 (USD). A yau, ma’auni ɗaya yana kai wa dalar Amurka 1,255.
“A shekarar 2017, tan daya na potash ya kai dalar Amurka 256. A yau tan guda ɗaya ya na kaiwa dalar Amurka 1,187.
“A cikin 2017, tan na Urea ya kasance dala 300. A yau tan ɗaya shine dalar Amurka 1,037.
“Kun ga cewa farashin kayayyakin taki a kasuwannin duniya ya tashi kuma wannan ya shafi har Najeriya,” in ji shi.