
Kwamatin dake kula da rabon arzikin kasa tsakanin Gwamnatin tarayya da Gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi (FAAC) ya tabbatar da cewar a cikin wata ukun farko na wannan shekarar Gwamnatocin sun kasafta Naira Tiriliyan 1.9 a tsakaninsu.
Bayanai sun nuna cewar an samu karin kashi 37.3 akan abinda aka raba a baya cikin wata ukun karshe na shekarar 2017, inda Gwamnatocn suka raba Naira Tiriliyan 1.411.
A wannan karon Gwamnatin tarayya ta samu zunzurutun kudi Naira biliyan 812.8 yayin da jihohi 36 suka kasafta Naira biliyan 683.4, haka suma Gwamnatocin kananan hukumomi sun rabauta da samun Naira biliyan 393.3 domin kasaftawa tsakaninsu.
Ko meye ra’ayinku game da yadda ake rabon wadannan kudade tsakanin Gwamnatoci, shin kwalliya tana biyan kudin sabulu?