Home Kanun Labarai Gwamnatin tarayya ta cewa Diezani ta sakata ta bararraje a London

Gwamnatin tarayya ta cewa Diezani ta sakata ta bararraje a London

0
Gwamnatin tarayya ta cewa Diezani ta sakata ta bararraje a London
Madam Diezani Alison-Madueke

Daga Abba Wada Gwale

Gwamnatin tarayya ta ce tsohuwar minister man fetur Diezani Alison-Madueke ta yi zamanta a birnin London don ci gaba da fuskantar shari’a.

Wannan bayanin yana fitowa ne ta bakin ministan shari’a Abubakar Malami lokacin da aka yi masa tambaya ko ƙasar nan za ta amince da buƙatar da Diezanin ta yi na a dawo da ita Najeriya domin a ci gaba da tuhumarta.

Ministan ya ce magana ake yi ta shari’a saboda haka haka gwamnatin Najeriya ba zata shiga hurumun gwamnatin Birtaniya ba.

Ya ƙara da cewa tunda tana fuskantar shari’a a can babu buƙatar sai an dawo da ita gida domin cigaban tuhumar da ake mata.

A ranar Talata nan ne dai tsohuwar ministan man fetur din a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Ebele Jonathan ta shawarci wata babbar kotu a jihar Legas da ta sa ministan shari’ar  ƙasar nan ya karɓi ragamar tuhumar da ake mata a ƙasar Birtaniya domin cigaba da yi a gida Najeriya.

Lauya Malami ya ƙara da cewa Najeriya tana da alaƙa mai kyau da ƙasashen duniya wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, musamman ƙasar Ingila, saboda haka batun a dawo da shari’ar da ake mata bai taso ba.

A karshe ya ce tunda gwamnatin Birtaniya ta yi nisa wajen binciken tsohuwar ministan hakan yasa dawo da ita bashi da wani alfanu.

Diezani dai tabar ƙasar nan tun shekarar 2015 bayan da gwamnatin PDP ta faɗi zaɓe inda ta koma ƙasar Ingila da zama.

Gwamnatin APC dai ƙarkashin mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta sha alwashin yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan.