Home Siyasa 2023: Gwamnatin Tarayya ta tura DSS, sojoji don tsaurara tsaro a ofisoshin INEC

2023: Gwamnatin Tarayya ta tura DSS, sojoji don tsaurara tsaro a ofisoshin INEC

0
2023: Gwamnatin Tarayya ta tura DSS, sojoji don tsaurara tsaro a ofisoshin INEC
Gwamnatin Tarayya ta tura jami’an tsaro na DSS da sojoji da jami’an hukumar kashe gobara ofisoshin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC domin tsaurara tsaro gabannin zaɓen 2023.
Gwamnatin ta kuma umarci jami’an su inganta tattara bayanan sirri domin daƙile duk wani yunƙuri na rikici ko ɓata gari a makonni masu zuwa gaba.
Babban Sufeta Janar na ‘yan sanda kasar, Usman Baba ne ya shaida hakan bayan tattaunawa da shugabanni jam’iyyun siyasa a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja.
Rundunar ta ce a cikin mako shida, an samu rigingimu aƙalla 52 a sassa daban-daban na ƙasar da suka haɗa da Ogun da Osun.
Akwai kuma harin da aka kai wa magoya-baya a gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohi irinsu Borno da Kaduna da Zamfara da dai sauransu.
Rundunar ta ce tana tsare da wasu da ake zargi na da hannu a waɗannan rikice-rikice, kuma za a gurfanar da su domin fuskantar hukunci.