
Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar ya shaidawa sashin Hausa na BBC cewar, gwamnoni, musamman na Jam’iyar APC ba sa tsoron ayi zaben ƴar tinƙe, wanda a ka fi sani da ƙato-bayan-ƙato.
Gwamnan ya baiyana cewar, damuwarsu ita ce yawan kuɗaɗen da za a kashe yayin gudanar da wannan zaɓen, domin a cewarsa “dole zaɓen zai ci kuɗi sosai, saboda yayi kama da zaɓen du-gari.
Ya ƙara da tambayar cewa, “a ina Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai Zaman Kanta, INEC zata samo kuɗaɗen da za ta gudanar da wannan zaben?”
Domin, a cewar gwamnan, idan an ce ko ina za a baiwa mutane dama su yi zaɓen to dole a ɗauki ma’aikatan zaɓe kuma dole a biyasu.