
Rahotanni sun nuna cewa Gwamnonin jam’iyyar APC a jiya Litinin, a wata ganawa da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, ya zabi mataimakin takararsa, Sanata Kashim Shettima.
Jaridar Punch ta rawaito cewa sai da shugaban kasa ya shiga tsakani domin tausar gwamnonin tare da hada kan su domin marawa tikitin Tinubu-Shettima a zaɓen 2023, lokacin da suka ziyarci gidansa na Daura.
Wasu majiyoyi a ganawar sirrin da shugaban kasar ya yi da gwamnonin APC su 9, sun shaida wa Punch cewa duk da cewa ɗan takarar na APC yana da ‘yancin zabar abokin takararsa, amma ba su kammala tattaunawa da Tinubun ba kafin ya bayyana zaɓin sa na Shettima.
Gwamnonin Arewa-maso-Yamma sun fi son Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu; ko takwaransa na Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; saboda karfin su na masu zaɓe a shiyyar.
Jaridar ta tattaro cewa gwamnonin sun fusata da jin cewa Tinubu din ya dauko Shettima. Tun da farko Tinubu ya bayyana a ranar Lahadi cewa bai ma sanar da Shettima matakin da ya dauka na zabar shi a matsayin abokin takararsa ba.
“A taron, gwamnonin sun nuna fushinsu kan matakin da Tinubu ya dauka na zabar Shettima. Kamar bai damu da ra’ayin gwamnoni ba duk da cewa zai dogara da su don yin gangami. Sai dai Buhari ya roke su da su karbi Shettima tunda shi dan jam’iyya ne mai aminci,” in ji wani mai taimaka wa daya daga cikin gwamnonin.
Wata majiya kusa da wani gwamnan Arewa maso Yamma ta ce gwamnonin duk sun yi mamakin sanarwar da Tinubu ya yi.
“Dukkanmu mun kalli sanarwar ne a talabijin kamar kowane dan Najeriya. Tinubu bai tattauna wannan da kowa ba. Har ma ya yarda bai sanar da Shettima shawarar da ya yanke na zabar shi a matsayin abokin takara ba. Wannan bai dace ba ko kadan kuma gwamnonin sun bayyana hakan,” inji shi.
Shi ma wani na hannun daman Tinubu ya ce bai kamata Tinubu ya bayyana hakan ba.
“Abin da ya faru shi ne kamar sanarwar da Tinubu ya yi a fadar shugaban kasa a watan Janairu lokacin da ya shaida wa manema labarai aniyarsa ta tsayawa takara. Wani lokaci, yana yin waɗannan sanarwar a cikin hanzari. Da yawa daga cikinmu sun kadu,” ya kara da cewa.